Rahotanni dake shigo mana yanzu haka daga Jihar Kano na bayyana cewar anyi nasarar damke wasu mutane wa?anda ake Zargi da safarar wata nau’in masara dake dauke da guba a Jihar Kano.
Shugaban hukumar ya?i da rashawa ta Jihar Kano Barista Mahmud Balarabe ya bayyana hakan lokacin da yake zantawa da manema labarai a birnin Kano.
Ya bayyana cewar sun yi nasarar kama mutum biyu kafin daga bisani suka samu kama na ukun, wanda bincike ya nuna cewar shi yake kula da wani Sito wanda aka tara masarar a ciki, kuma tuni an dauki samfarin masarar domin gudanar da bincike a kai.
Da yake jawabi akan lamarin Malam Murtala Inuwa na Hukumar kula da cimaka ta Jihar, ya bayyana cewar shigowar wannan masara garin Kano ba karamin tashin hankali bane, kuma lallai za suyi dukkanin mai yiwuwa wajen da?ile wanzuwar ta cikin jama’a.
Sai dai anashi ?angaren Shugaban kasuwar hatsi ta Dawanau Alhaji Sani Adam ya bayyana cewar ba wai guba bane a jikin Masarar sai dai masarar ta rube ne, kuma wadanda suke da ita suke ganin maimakon su yi asara gwamma su karya farashin ta su samu kudi, amma a yadda masarar take ko dabba ba zai iya ci ba ballantana Mutum.
