Rahoton dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Babban Sufetan ‘Yan Sanda na kasa, Alkali Baba Usman yana rigima da hukumar PSC mai kula da aikin ‘yan sanda a dalilin shirin daukar aiki na sabbin jami’an ‘yan sanda.
An ruwaito hukumar PSC ta bude shafin yanar gizo ga masu neman aikin ‘dan sanda. Bayan hukumar ta bada sanarwar daukar aiki na shekarar nan ta 2022, sai rundunar ‘yan sanda ta bada sanarwar ayi watsi da maganar daukar aikin.
A wani jawabi da jami’in hulda da jama’a na ‘yan sandan Najeriya, CSP Olumuyiwa Adejobi ya fitar yana cewa babu shirin daukar aiki, hukumar PSC ba ta da alaka da daukar aikin rundunar ‘yan sanda na kasa.
Kakakin ya yi magana a Twitter, yana cewa babu abin da ya hada sanarwar da hukumar PSC ta fitar da shirin daukar aikin sababbin jami’ai.
“Rundunar ‘yan sandan Najeriya ta na sanar da jama’a cewa ba a soma fara daukar aikin kurata domin shiga aikin ‘yan sanda na shekarar 2022 ba.
