An bayyana jihohin Kano Bauchi da Kebbi a matsayin jihohin da ake mumunar magudin satar jarabawar kammala karatun Sakandare a fadin tarayyar Najeriya.
Shugaban hukumar Jarabawa takasa, NECO, Dantani Wushishi ne ya bayyana haka,Wushishi ya bayyana hakan ne a jawabin da ya gabatar a taron shugabannin makarantun dake hada karatun Boko da na Islamiyya mai take, ‘Illar magudin zabe: Magance matsalar don cigaban kasa.
Ya kara da cewa magudi da satar amsa a jarabawa sun yi muni a Arewacin Najeriya amma abin ya fi muni a jihohin Kano,Bauchi, Borno da Kebbi a shekaru 5 da suka gabata.
