Rahotanni dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewa tsohon Gwamnan Jihar Jigawa Sule Lami?o ya bayyana cewa kwata-kwata ba shi goyon bayan maida mu?aman siyasa zuwa tsarin kar?a-kar?a, saboda babu wata tsiya da kar?a-kar?a ya tsinana wa ?asar nan.
Lami?o wanda ya yi gwamna tsawon shekaru takwas a Jigawa, bayan ya zama Ministan Harkokin Waje daga 1999 zuwa 2003, ya ta?a yin takarar shugabancin ?asa a 2019.
Tsohon gwamnan wanda su ne su ka ?afa PDP, ya shaida wa BBC Hausa a ranar Asabar cewa tsarin kar?a-kar?a bai tsinana komai ba.
“Idan PDP ta zo ta ce a yi tsarin kar?e?eniyar shugabancin Najeriya, zan ce masu a’a. Saboda yadda duniya aka ci gaba a yanzu, tuni an wuce batun kar?a-kar?ar shugabancin. Maganar da ake yi a duniya kawai ita ce yadda za a ci gaba a bun?asa.
