Makarantu 14 Na Fuskantar Barazanar Satar Dalibai Daga ‘Yan Bindiga

IMG 20240312 WA0021

Hajiya Halima Iliya, shugabar shirin samar da ku?a?en bayar da kariya ga makarantu na ?asa, ta ce hukumar ta tattara bayanai da za su taimaka wajen kai wa makarantun ?auki.

A shekarar 2014 ne aka kafa hukumar bayan sace ?aruruwan ?aliban makarantar Chibok da ke jihar Borno a arewa-maso-gabashin ?asar.

Jihohin da wasu makarantunsu ke cikin ha?arin sun ha?a da Adamawa, Bauchi, Borno, Benue, Yobe, Katsina, Kebbi, Sokoto, Filato, Zamfara da birinin Abuja. A cewar hukumar.

A ranar Alhamis da ya wuce ne ?anbindiga suka sace ?alibai 270 na makarantun firamare da sakandire a ?auyen Kuriga da ke jihar Kaduna.

Haka kuma a ranar Asabar da ta wuce ne wasu ?anbindigar suka sace ?aliban makarantar tsangaya kimanin 15 a ?aramar hukumar Gada a jihar Sokoto.

Sace-sacen sun biyo bayan sace wasu ?aruruwan ?angudun hijira a Ngala da ke jihar Borno da ake zargin ?anBoko Haram da aikatawa.

Iyaye da ?an’uwan ?alibai da sauran wa?anda aka sacen na ci-gaba da ro?on gwamnati ta ku?utar da su.

Related posts

Leave a Comment