Fadar Shugaban kasa ta musanta zargin yin coge a kasafin kudin 2024 wanda Shugaban kasar ya sanyawa hannu a watan Janairu.
?angaren zartarwar ta mayar da martani ne kan wata hira da BBC ta yi da shugaban ?ungiyar ?anmajalisar dattawan ?asar na yankin arewa, Sanata Abdul Ningi wanda ya yi zargin cewa kasafin ku?in da bangaren zartarwa ke aiki da shi ba shi ne majalisun dokokin kasar suka rattabawa hannu ba.
Sai dai mataimaki na musamman ga shugaban kan watsa labarai, Abdulaziz Abdulaziz ya ce ba kamshin gaskiya a zargin.
