Rundunar ‘yan sandan jihar Ogun ta tabbatar da sace ma’aikatan Gonar Obasanjo Holdings guda uku da wasu ‘yan bindiga da ba a san ko su waye ba suka sace su a kan babbar hanyar Kobape zuwa Abeokuta.
An ruwaito cewa kakakin rundunar, Abimbola Oyeyemi ya bayar da tabbacin ne a Abeokuta, yayin tabbatar da faruwar lamarin, ya ce an sace mutanen ne, a ranar Laraba, 8 ga Satumba, da misalin karfe 6 na yamma, a Kauyen Seseri, kusa da Kobape.
Rundunar ‘yan sandan ta ba da tabbacin cewa jami’an ta za su yi duk mai yiwuwa wajen ganin sun ceto ma’aikatan daga hannun ‘yan Bindigan.
A halin da ake ciki, ana kyautata zaton an shiga da ma’aikatan cikin daji, inda aka boye su a wani wurin da ba a sani ba.
An ruwaito cewa wadanda aka sace sun hada da mai kula da harkokin kudi, shugaban kididdiga na kudi da manajan ma’ajiyar kamfanin, wanda aka ce mallakar tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo ne.
Rahotanni sun bayyana cewa, ‘yan bindigan sun yi musu kwanton bauna ne yayin da suke tuka mota kirar Toyota Hilux a kan wata babbar hanya. Kakakin rundunar na Ogun yace: “Sace mutanen ya faru ne da misalin karfe 6 na yamma.
“Mutanen mu sun fara neman su kuma za mu tabbatar an kubutar da su.” Kakakin rundunar ‘yan sandan ya nanata kudirin rundunar na tabbatar da tsaron rayuka da dukiyoyi a jihar.
