Majalisar Dattawa Ta Zabi Jagororin Majalisa

Rahotannin dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Shugaban Majalisar Dattawa Sanata Godswill Akpabio ya sanar da manyan Majalisar ta 10 a jam’iyyarsu ta APC – ?angaren masu rinjaye ke nan.

Haka nan ya sanar da na marasa rinjaye, wato na jam’iyyun adawa.

Ga yankunan da na masu rinjaye suka fito:

Sanata Opeyemi Bamidele – Shugaban Masu Rinjaye daga Jihar Ekiti (kudu maso yamma)
Sanata David Umahi – Mataimakin Shugaban Masu Rinjaye daga Jihar Ebonyi (kudu maso gabas)
Sanata Ali Ndume – Mai Tsawatarwa na Masu Rinjaye daga Jihar Borno (arewa maso gabas)
Sanata Lola Ashiru – Mataimakin Mai Tsawatarwa na Masu Rinjaye daga Jihar Kwara (arewa ta tsakiya)
Yankunan da na marasa rinjaye suka fito:

Sanata Simon Davou na PDP – Shugaban Marasa Rinjaye daga Jihar Filato (arewa ta tsakiya)
Sanata Oyewunmi Olarere na PDP – Mataimakin Shugaban Marasa Rinjaye daga Jihar Osun (kudu maso yamma)
Sanata Darlington Nwokeocha na LP – Mai Tsawatarwa na Marasa Rinjaye daga Jihar Abiya (kudu maso gabas)
Sanata Rufai Sani Hanga na NNPP – Mataimakin Mai Tsawatarwa na Marasa Rinjaye daga Jihar Kano (arewa maso yamma)

Related posts

Leave a Comment