Majalisar masarautar Zazzau ta amince da dakatar da Marafan yamman Zazzau bayan wani zama da ta yi a ranar Litinin.
A wata sanarwa da ta samu sa hannun mai magana da yawun masarautar, Abdullahi Aliyu Kwarbai, ta ce matakin ya biyo bayan samun basaraken da laifin ?aukar doka a hannun shi.
Sanarwa ta ?ara da cewa: “A sakamakon haka, Majalisar Masarautar Zazzau ta amince cikin gaggawa da dakatar da Alhaji Mustapha Adamu Ubaidu, Marafan Zazzau daga masarautar har sai abin da hali ya yi.”
Dakatarwar, kamar yadda sanarwar ta nuna ta biyo bayan koken da al’ummar Unguwar Magajiya da ke cikin birnin suka kai wa majalisar.
Masarautar ta ce a shirye take ta ?auki tsauraran matakai kan masu ri?e da mu?amai wa?anda ke sa?a wa doka, inda ta bu?ace su da su mi?a duk wani batu da ya shafi hukunci ga mahukunta.
