Rahotannin dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Majalisun tarayya sun kada kuri’ar kin amincewa da bai wa shugabannin majalisar rigar kariya tare da yin watsi kara yawan mata a majalisun tarayyar kasar.
An dai kada kuri’ar kan kudurorin yi wa tsarin mulkin kasar na 1999 gyaran fuska ta hanyar na’ura, inda galibin ‘yan majalisun suka sami matsaya kan abubuwan da aka rika ce-ce-ku-ce akansu.
Tuni kungiyoyin mata suka fara nuna bacin ransu kan kin amincewa da mahimman bukatun da suka shafisu.
Kudirori sittin da takwas ne aka kada kuri’a akansu, inda ‘yan majalisar suka ki amincewa da batun bai wa shugabannin majalisun tarayyar da cif joji-jojin kasar rigar kariya da kuma kin amincewa da bai wa mata kashi goma sha biyar cikin dari na shugabancin jam’iyyu.
Sai dai ‘yan majalisar sun amince da bai wa kananan hukumomi ‘yancin gashin kansu.
