INEC Ta Fitar Da Jadawalin Za?en Shekarar 2023

Rahoton dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Hukumar Za?e ta ?asa (INEC) ta buga sanarwar shirye-shirye da jadawalin ranakun za?en 2023, kamar yadda dokar za?e ta tanadar ta yi.

INEC ta bayyana shirye-shiryen ciki har da batun sayen fam da inda za a saye shi, yadda za a cike fam da kuma inda za a mayar idan ?an takara ya cike.

Daraktan Wayar da Kan Masu Za?e Victor Aluko ne ya bayyana haka a Abuja, a ranar Litinin.

INEC ta ce an li?a sanarwar lokuta da ranakun za?e da batun sayen fam a kowane ofishin INEC na kowace jiha a fa?in ?asar nan, har da Abuja.

Sanarwar ta umarci duk,mai sha’awar shiga takara idan ya sayi fam, to ya cike ya aika shi kai-tsaye Hedikawar INEC da ke Maitama, Abuja, ta hanyar shiga rumbun bayanan INEC da aka ware musamman don hakan.

Related posts

Leave a Comment