Rahotanni daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Shugaban ?asa Muhammadu Buhari ya isa Nairobi babban birnin ?asar Kenya domin halartar taron hukumar kula da muhalli ta Majalisar ?inkin Duniya UNEP da ke cika shekara 50 da kafuwa.
Fadar shugaban ta ce a yau Talata 1 ga Maris Buhari ya tafi Kenya domin halartar bikin hukumar UNEP na kwana uku tsakanin 3 zuwa 4 na Maris.
Shugaban zai tafi tare da rakiyar ministocinsa na harakokin waje da na muhalli da kuma mai ba shi shawara kan sha’anin tsaro.
Daga nan shugaban zai tafi London domin diba lafiyarsa, kuma zai shafe tsawon mako biyu, a cewar sanarwar da fadar shugaban ta fitar.
