A yayin da ta?addama ke cigaba da gudana a sassan Najeriya akan inda ya kamata mulki ya koma a Shekarar 2023 tsakanin Arewaci da Kudancin Najeriya, Wanda ya kirkiro tsohuwar jam’iyyar CPC, Sanata Rufai Hanga, ya ce akwai bayyanannen yarjejeniya cewa Buhari zai mika mulki hannun shugaban jam’iyyar APC kuma tsohon gwamnan jihar Legas, Asiwaju Ahmed Bola Tinubu a 2023.
Hanga wanda ke shugabantar daya daga cikin tsoffin jam’iyyun da suka hade suka zama APC a 2014 ya sanar da hakan a wata tattaunawa da yayi da manema labarai a birnin tarayya Abuja.
Inda yayin bayanin cewa wannan yarjejeniyar ce dalilin da yasa Tinubu yake APC bayan kammala wa’adin Buhari na farko.
“Wannan bayanannen sirri ne. Akwai yarjejeniya kuma a bayyane. Sun yi yarjejeniyar cewa Tinubu zai karba mulki, Hakan ce ta sa bai bar jam’iyyar ba tun a karon farko na mulkin Buhari.
Da a ce Tinubu ya san ba zai samu komai ba, da ya zare jikinsa tun mulkin karon farko. Amma ya san akwai yarjejeniya,” kuma yana sa ran a cika mishi alkawari.
Sanata Hanga ya nuna tantamarsa na cewa ko jam’iyyar APC za ta baiwa Tinubu tikitinta, lamarin da yace zai iya kawo hargitsi da kishin neman mulki daga wasu gwamnoni da makusantan shugaban kasan.
Tsohon dan majalisar ya ce duk da manyan jam’iyyu biyun suna da nasu matsalolin, zai yuwu ‘yan Najeriya su koma bayan PDP sakamakon rashin kwazon da jam’iyyar APC ta nuna karkashin mulkin shugaba Buhari.
