Rahotanni daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Majalisar Dattawa ta amince da sabbin ministoci bakwai da shugaba Muhammadu Buhari ya tura ma ta domin tabbatar da na?insu.
An tabbatar da na?in ne bayan zaman tantace su da majalisar ta yi a zamanta na wannan Larabar.
Yayin da wasu daga cikin sabbin ministocin, musamman tsohon ?an majalisa, da aka bukaci su yi gaisuwar majalisa su wuce, wasu daga cikinsu an tsare su da tambayoyi kan abubuwan da ya shafi kasa.
Shugaba Buhari, a wata wasika da ya aikewa majalisa mai dauke da kwanan watan 15 ga watan Yuni, 2022, ya bukaci majalisar ta amince da na?insa.
Ya ce neman bukatar amincewa da na?in ya yi daidai da tanadin kudin tsarin mulki sashi na 147(2) na kudin tsarin mulkin shekara ta 1999 na Tarayyar Najeriya, da aka yiwa kwaskwarima.
Ministocin da aka tabbatar da na?in nasu sun ha?a da: Henry Ikechukwu Ikoh daga Abia; Umana Okon Umana daga Akwa Ibom; Ekumankama Joseph Nkama- daga Ebonyi; da Goodluck Nanah Opiah daga Imo.
Sauran su ne Umar Ibrahim El-Yakub daga Kano; Ademola Adewole Adegoroye daga Ondo; da Odum Udi daga Rivers.
