2023: Atiku Na Fuskantar Barazanar Cikin Gida

Labarin dake shigo mana yanzu haka daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Tsohon gwamnan jihar Ekiti, Ayodele Fayose, ya bu?aci mulki ya koma kudancin Najeriya, a cewarsa babu adalci wani ?an arewa ya kar?i mulki bayan shugaban ?asa, Muhammadu Buhari, ya kammala wa’adi biyu.

Fayose, na hannun daman gwamnan Ribas Nyesom Wike, yana ?aya daga cikin yan takarar da suka fafata a za?en fidda gwanin PDP, wanda tsohon mataimakin shugaban ?asa, Atiku Abubakar, ya lashe.

A wani rubutu da ya fitar a shafinsa na Tuwita ranar Laraba, Fayose ya ce yanzu lokaci ne na kudancin Najeriya ya samar da shugaban ?asa na gaba, ba tare da ?ata lokaci ba.

“Kwansutushin ?in PDP ya tanadi tsarin karba-karba a kujerar shugaban ?asa. Sashi na 3 (c) ya tanadi cewa jam’iyya zata cika manufofinta ta hanyar tsayuwa kan tsarin karba-kar?a, yanki-yanki game da kujerun jam’iyya da na za?e don tabbatar da adalci da dai-daito.”

“Shugaban ?asa na yanzun ?an arewa ne da zai kammala wa’adinsa biyu, hakan na nufin wajibi kujerar shugaban ?asa ta koma kudanci a 2023 ko bakomai.”

Related posts

Leave a Comment