Majalisa Ta Amince Da Nadin Sabbin Hafsoshin Tsaro

Majalisar Dattawa ta amince da na?in da shugaban ?asa Bola Ahmed Tinubu ya yi wa manyan hafsoshin sojin ?asar.

Amincewar ta biyo bayan tantance hafsoshin da aka yi a zauren majalisar ranar Alhamis.

Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio ya ce a lokacin tantancewar, wadda aka yi a asirce, hafsoshin sojin sun amsa tambayoyi kan lamurran da suka shafi tsaro da kuma halin da ?asar ke ciki.

A ranar Litinin, Shugaban Tinubu ya aika wa majalisar da wata takarda yana bu?atar amincewa kan na?in da ya yi wa manyan hafsoshin.

Manyan hafsoshin da aka amince da na?in nasu su ne:

1-Manjo-Janar C.G Musa (Hafsan hafsoshin dakarun Najeriya)
Manj-Janar T. A Lagbaja (Babban hafsan maya?an ?asa)

2-Rear Admiral E. A Ogalla (Babban hafsan maya?an ruwa)
AVM H. B Abubakar (Babban hafsan maya?an sama)

3-IGP Kayode Agbetokun (Mai ri?on mu?amin Sufeta-Janar na ?an sanda)

4-Manjo-Janar EPA Unidianye (Shugaban Hukumar Tattara bayanan sirri na tsaron kasa

Related posts

Leave a Comment