Hukumar tsaron farin kaya DSS ta gurfanar da dakataccen Gwamnan Babban Banki Godwin Emefiele a gaban kotun.
Cikin wata sanarwa da mai magana da yawun hukumar Peter Afunaya ya fitar, ya ce hukumar ta gurfanar da Mista Emefiele a gaban kotun ne domin bin umarnin babbar kotun tarayya da ke Abuja da ta bayar da ta umarci hukumar ta DDS da kai shi kotu domin tuhumarsa ko kuma ta sake shi.
Sanarwar ta ambato Mista Afunaya na cewa tun shekarar 2022 ne, hukumar DSS ta nemi umarnin kotu domin tsare Emefiele don gudanar da bincike kan wasu manyan laifuka da ka zarge shi da aikatawa.
Ranar Laraba ne dai wata Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta umarci hukumar tsaron farin kaya ta tuhumi Godwin Emefiele a kotu cikin mako ?aya ko kuma ta sake shi.
Mista Emefiele ne dai ya shigar da ?arar don tabbatar da ‘yancinsa na ?an’adam, inda yake ?alubalantar kamawa da tsare shi da Hukumar DSS take yi.
A ranar 10 ga watan Yuni ne Hukumar DSS ta ba da sanarwar cewa ta kama tare da tsare, Godwin Emefiele, kwana guda bayan shugaban ?asar ya dakatar da shi.
Tsohon shugaban Najeriya Goodluck Jonathan ne ya na?a Emefiele a matsayin shugaban CBN a shekarar 2014.
Ya ci gaba da zama shugaban babban bankin na Najeriya har ?arshen wa’adin mulki na biyu na tsohon shugaban ?asa Muhammadu Buhari.
Sai dai wasu matakai da ya ?auka gabanin babban za?en Najeriya na 2023 ya janyo ce-ce ku-ce mai yawa a ?asar.
Batun sauya fasalin ku?i da bankin ya ?addamar ya haifar da ?arancin ku?i a hannun al’umma, wani abu da ya janyo wahalhalu da dama.
Sai dai Emefiele ya ce sauya fasalin ku?in wani yun?uri ne na ya?i da rashawa da matsalar tsaro da kuma ?abba?a tsarin rage amfani da tsabar ku?i tsakanin al’umma.
Amma wasu daga cikin makusantan
