Wata wasika da kungiyar ta rubutawa ministan makamashi, ta bayyana matukar damuwarta da karin a kasar inda tace an samu tsadar kayayyakin abinci da kuma harkokin yau da kullum.
Wasikar da Sakatare Janar na kungiyar Dominic Igwebike ya sa wa hannu tace karin kudin zai sa wasu ‘yan Najeriya dake da hannu da shuni su koma sayen kayayyakin da ake sarrafawa a kasashen ketare, domin kamfanonin gida ba zasu iya sarrafa masu inganci ba saboda hauhawan farashi.
Igwebike ya kuma ce wannan zai iya sanya wasu kamfanonin da ba zasu iya gogaiya ba rufewa baki daya.
Sakataren ya kuma bayyana cewar karin na iya jefa rayuwar ma’aikatan wutar cikin hadari, sakamakon arangama da fusatattun mutanen da ake zuwa yankewa wutar saboda gaza biyan kudin wutar da suke sha.
