Rahotannin dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewa ?ungiyoyin ?wadago sun gabatar da mafi ?arancin albashi da suke so gwamnati ta biya ma’aikata a duk ?arshen wata.
?ungiyoyin na TUC da NLC sun cimma matsayar N615,000 a matsayin sabon mafi ?arancin albashi da suke son ma’aikata su ri?a samu, wannan matsayar dai tuni suka sanar da gwamnati bayan sun kammala tattaunawa a tsakaninsu.
An ruwaito wani babba ne a ?ungiyar ?wadago da ya nemi a sakaya sunansa shi ne ya tabbatar da cewa N615,000 a matsayin mafi ?arancin albashin.
Majiyar wanda yana cikin kwamitocin da gwamnati ta kafa domin samar da sabon mafi ?arancin albashin, ya ce ku?in za su iya ?aruwa biyo bayan ?arin ku?in wutar lantarki da aka yi.
“Mu a NLC da TUC mun mi?awa gwamnati abin da muke bu?ata kan mafi ?arancin albashi wanda shi ne N615,000. Wannan ita ce matsayar TUC da NLC kan batun. Mun sanar da gwamnati hakan.”
