Ma’adinan Karkashin Kasa Dake Arewa Ne Silar Ta’addanci A Yankin – Kwankwaso

?an takarar shugaban kasa a inuwar Jam’iyyar NNPP, Rabiu Kwankwaso, yace fafutukar neman ma’adan kasa ne asalin abinda ya haifar da ta’addanci a arewa maso yamma da arewa maso gabas.

Kwankwaso ya bayyana haka ne yayin da yake jawabi a Chatham House da ke birnin Landan na ?asar Burtaniya ranar Laraba, kamar yadda jaridar Punch ta ruwaito.

Tsohon gwamnan jihar Kano kuma tsohon Ministan tsaro yace mutane daga ciki da wajen Najeriya ke “Satar” ma’adanai shiyasa ya?i ya turnuke yankunan.

“A ?asata Najeriya muna da tsarin lada da kuma tsarin hukunci saboda a halin yanzun komai ya wuce. Lokacin ina gwamnan Kano, ba wanda zai je da sunan gwamnati ya karbi harajin ?wandala ?aya.” “Tsawon shekaru 8 da na kwashe kan madafun iko ban karbo bashin ko kwabo ba, abinda muka maida hankali shi ne albarkatun jiharmu, shiyasa wasu mutane ke tambayar wai ina muke samun ku?in shiga.”

“Ya?e-ya?en da ake a arewa maso yamma da arewa maso gabashin Najeriya duk kan ma’adanan ?asa ne, mutane na sace su daga cikin Najeriya da waje, ciki harda Gwal da sauran ma’adanai.” Kwankwaso ya ce lokacin ya yi da wannan matsalar zata kau, gwamnati ta ?wace wadannan Arzikin da Allah ya bamu domin yi wa yan kasa aiki.

Bugu da kari, tsohon gwamnan yace Najeriya ta wayi gari cikin wannan bakin yanayin ne sakamakon gurbataccen shugabanci da kuskuren zabe.

Related posts

Leave a Comment