Ministan harkokin ‘yan sanda Mohammed Maigari Dingyadi, ya ce babban sifeton ‘yan sandan ?asar Usman Baba Alkali, ba zai yi ritaya a lokacin tsakiyar za?ukan ?asar da ke tafe, kamar yadda ake tsammani.
Ministan na wannan maganar ne yayin da yake amsa tambayar manema labarai a fadar gwamnatin ?asar jim ?adan bayan kammala taron majalisar zartawar ?asar.
Dingyadi – wanda ya ce tuni babban sifeton ‘yan sandan ya kar?i takardar tsawaita aikinsa – ya ?ara da cewa sabuwar dokar aikin ‘yan sanda ta 2020 ta sauya tsarin ritayar sifeton ‘yan sandan.
Wasu kafofin ya?a labarai sun ruwaito cewa babban sifeton zai cika shekara 60 ranar 1 ga watan Maris mai zuwa kwanaki kwana hu?u bayan za?en shugaban ?asar.
To sai dai yayin da yake amsa tambayar ‘yan jarida kan ko akwai yiyuwar babban sifeton ‘yan sandan zai yi ritaya a lokacin, sai ministan ya ce ”ban san inda kuka samo wa?annan bayanai ba”
”To amma bari na fa?a muku dokar aikin ‘yan sanda ta 2020 ta nuna cewa nan gaba babban sifeton ‘yan sanda zai ?ara shekara hu?u a kan mu?aminsa, kuma tuni shugaban ?asa ya ba shi takardar tsawaita wa’adinsa, dan haka batun saukar Sifeton ‘yan sanda a lokacin tsakiyar za?ukan ?asa bai taso ba”, in ji ministan
