Ambaliyar Ruwa: Manoman Jihar Adamawa Sun Bukaci Agajin Gwamnati

Manoma a Jihar Adamawa sun bukaci gwamnatin tarayya da jihar da su taimaka musu biyo bayan ambaliyar ruwa da yayi sanadiyar salwantar gonakinsu da dama tare da yin asarar dukiyoyi masu yawa.

Shugaban Kungiyar manoma na Yankore dake Jambutu a cikin karamar hukumar Yola ta Arewa fadar gwamnatin jihar Adamawa, Alhaji Abdulrazak Abubakar ne yayi wannan kira a zantawarsa da Wakilinmu a Yola.

Abdulrazak Abubakar yace ambaliyar ruwa yaci musu gonaki da dama tare da gidaje don haka ya zama wajibi su kirayi gwamnatin tarayya dana jihar da suyi wa Allah da manzonsa su kai musu ?auki domin rage musu ra?a?in asara da suka yi.

Ambaliyar ruwan dai ya shafi kananan hukumomi da dama a jihar Adamawa wanda yayi sanadiyar salwantar dukiyoyi masu yawa.

Tunda farko dai hukumar hassashen yanayi ta Najeriya ta ayyana jihar Adamawa na daya daga cikin jihohi da zasu fuskanci ambaliyar ruwa a wannan shekara.

Related posts

Leave a Comment