?an takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC, Bola Tinubu ya zargi dan takarar shugaban kasa na PDP Atiku Abubakar da sharara karya game da abubuwan da suka faru a siyasa a baya.
An ruwaito labarin yadda Atiku ya yi tir da takarar Muslim-Muslim wanda APC ta yi, cewa APC ba ta yi wa ?an Najeriya adalci ba
Atiku ya ce ya yi mamakin da APC za ta za?i wannan baibawan-burmin siyasa, a ?asa kamar Najeriya mai mabiya addinai da al’adu ba ?aya ba.
Haka Wazirin Adamawa ya bayyana a tattaunawa da Gidan Talabijin na Arise TV ta yi shi a ranar Juma’a.
A ranar 10 Ga Yuli ne Bola Tinubu ya bayyana sunan tsohon Gwamnan Jihar Barno, Kashim Shettima a matsayin mataimakin takarar sa.
TInubu da Shettima duk Musulmai ne, lamarin da ya haifar da ce-ce-ku-ce a fagen siyasar Najeriya.
Atiku ya ce batun tikitin Muslim-Muslim shi ne kusan kandagarkin da ya yi masa katanga da Tinubu, shekaru da da?ewa tun ma kafin kafa APC.
Atiku ya bayyana yadda ya ?i goyon bayan a yi tikitin ‘Muslim-Muslim’, lokacin da za?en 20215 ya zo.
“Ni ban yarda a ce daidai ne a ?asa kamar Najeriya mai ?abilu da addinai mabambanta, amma a ce wai a fitar da ?an takarar shugaban ?asa da ?an takarar mataimakin shugaban ?asa duk Musulmai.” Inji Atiku.
