Rahotanni daga birnin Ikko na Jihar Legas na bayyana cewar gwamnatin Jihar ta ce tana bincike kan wani bidiyo da ya kara?e shafukan zumunta inda wasu ke raba man fetur a cikin jarkuna a matsayin kyautar halartar biki.
Kwamashinan Ya?a Labarai na jihar Legas, Gbenga Omotoso, ya ce “shakka babu wannan lamarin abin ha?ari ne kuma zai iya jawo rasa rayuka da dukiyoyi”.
A ‘yan awannin da suka gabata ne bidiyon ya ?ulla, inda aka ga jarkunan fetur masu lita 10 a jere da za a raba wa mahalarta bikin. An ce Chidinma Pearl Ogbulu ce ta shirya taron don murnar na?a ta a matsayin Erelu Okin.
Yanzu haka jama’a na fama da ?arancin man fetur, inda suke shafe awanni masu yawa a kan dogayen layuka.
