Tsohon shugaban ?asa Cif Olusegun Obasanjo ya ce wasu masu burin zama shugaban ?asa a za?en 2023 ya kamata a ce suna gidan yari idan da hukumomin da ke ya?i da rashawa a Najeriya suna aikinsu yadda ya dace.
Tsohon shugaban ya fa?i haka ne a wani babban taron ?ara wa juna sani da aka gudanar a Abeokuta jihar Ogun domin bikin cikarsa shekara 85 da haihuwa, kamar yadda jaridar The Punch ta ruwaito.
“Na kalli wasu daga cikin mutanen da ke yawo da kuma wadanda mutane ke yawo da su. Idan da EFCC da ICPC za su yi aikinsu yadda ya kamata da kuma goyon bayan ?angaren shari’a, da yawancinsu suna gidan yari.”
Duk wanda da ba ya da gaskiya a ?ananan abubuwa ba zai iya gaskiya ba manyan abubuwa,” in ji Obasanjo.
Tsohon shugaban ya kuma ce babu wani ?an takara a yanzu da yake goyon baya, duk da ya ce wasu daga cikin masu neman takarar shugaban ?asa sun kai masa ziyara suna neman goyon bayansa.
Obasanjo ya kuma ?aryata rahotannin da suka lissafa wasu ?an takara a yankin kudu da yake marawa baya.
“A irin wannan hali da muke ciki, ba zan yi gaggawar fa?in sunaye, ba tare da tuntu?a ba da kuma tabbatar da ingantattun ka’idoji da matakai ba,” in ji shi.
