Saudiyya Ta Janye Takunkumin Hana ‘Yan Najeriya Shiga Kasar

Rahotanni daga birnin Riyadh na kasar Saudiyya na bayyana cewar Gwamnatin kasar ta ?age haramcin hanawa ?an Najeriya shiga ?asarta saboda annobar korona.

Matakin ya shafi ?asashen Afghanistan da Afirka Ta Kudu da Namibia da Botswana da Zimbabwe da Lesotho da Eswatini da Mozambique da Malawi da Mauritius da Zambia da Madagascar da Angola da Seychelles da Comoros da kuma Ethiopia.

Sanarwar hakan na kunshe ne a cikin shafin hukumomin da ke kula da Masallatai biyu masu daraja na Ka’abah dake Makkah da Masallacin Annabi dake Madinatu Munawwarah.

Wannan na zuwa bayan sanar da ?age dakatar da Umrah, shekara biyu bayan dakatar da aikin Ibadar saboda annobar korona.

Related posts

Leave a Comment