Labarin dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan ya bayyana yadda gwamnatinsa a cikin kwana daya ta magance yajin aikin wata hudu da kungiyar malaman jami’o’i ASUU ta taba yi.
Ya bayyana hakan ne a ranar Laraba wurin bikin cikar Bishop Mathew Kukah shekaru 70 da haihuwa da aka yi a Cibiyar Kukah da ke birnin tarayya Abuja.
Kungiyar Malaman Jami’o’i a Najeriya sun fara yajin aiki tun watan Fabrairu kan rashin cika musu bukatunsu da gwamnatin tarayya ba ta yi ba, lamarin da ya jefa dalibai cikin mawuyacin hali a kasar.
“Tafiyar da kasar da muke ciki abu ne mai sarkakiya, yanzu muna maganan yajin aikin ASUU, nima lokaci na, ASUU ta yi yajin aiki na wata hudu, kwamiti daban-daban suna ta taro amma abin bai warware ba. Na ce ta yaya yaranmu za su zauna a gida na wata hudu? Sai na kira taron dukkan shugabannin ASUU.
“Ni na jagoranci taron tare da mataimaki na, Antoni Janar yana wurin, na ce dole mu warware matsalar a cikin daren nan. Sakataren Gwamnatin Tarayya yana wurin, ministocin ilimi suna wurin, ministocin kudi da kwadago suma suna wurin, dole kowa ya yi.
“Kuma ina ganin kasancewa ta a wurin ya taimaka mana kammala abin da wuri. Amma fa sai karfe 5.30 na asubahi muka kammala kuma aka janye yajin aiki, don haka akwai batutuwa.”
