Labarin dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar a ranar Laraba, 14 ga watan Satumba 2022, babban kotun tarayya da ke zama a garin Abuja za ta saurari karar da aka shigar a kan tikitin PDP a 2023.
An ruwaito cewa Alkalin Kotun Ahmed Mohammed ya zabi wannan rana domin ya cigaba da sauraron karar bayan an nemi karin lokaci.
Tun farko Lauyar da ta tsayawa Gwamna Aminu Waziri Tambuwal, Atiku Abubakar da jam’iyyar PDP, Prisicila Eje ce ta bukaci kotu ta kara musu lokaci.
Ganin Lauyan da ya shigar da kara, Wilfred Okoi bai da ja a kan wannan bukata, Mai shari’a Ahmed Mohammed ya amince a dawo nan da makwanni biyu.
A farkon watan Yuli aka fara shigar da wannan kara mai lamba FHC/ABJ/CS/782/2022, ana rokon kotun tarayyar ta hana Atiku tsayawa takara a za?en dake tafe na 2023.
Atiku Abubakar a Kano Hoto: Abban Hajia Asali: Facebook Rahoton yace hukumar INEC ba ta iya turo Lauyan da ya kare ta a zaman kotun da aka yi yau ba.
Bukatar Lauyan da ya kai kara sun hada da ayyana Gwamna Wike a matsayin asalin ‘dan takarar shugaban Najeriya na jam’iyyar PDP a zabe mai zuwa.
Duk da Wike ya yi ikirarin babu hannunsa a wannan kara da ke kotu, Lauyan da ya wakilci Gwamnan da kuma jagoran jam’iyyar PDP bai nuna haka ba.
