Gwamnatin Jihar Gombe karkashin jagorancin Gwamnan Jihar Alhaji Muhammad Inuwa Yahaya, ta amince da fara biyan daliban gaba da sakandiri kudin Scholarship, bayan shafe sama da shekaru ba a biya su ba.
Daliban Jihar Gombe sun tsunduma cikin farin ciki bayan jin wannan labarin.
Wannan mataki da gwamnatin Jihar Gombe ta dauka zai taimaka wajen rage ra?adin da dalibai da iyayen ?alibai musamman ta la’akari da halin da aka shiga ciki tun bayan ?arkewar cutar nan ta CORONA.
Jama’a da dama da aka zanta da su dangane da wannan mataki da gwamnan ya dauka, sun yaba gami da jinjinawa gwamnan tare da fatan sauran takwarorinshi za su ?auki sahu.
