Kwankwaso Ya Ja Kunnen ‘Yan PDP Kan Rikicin Cikin Gida

Tsohon gwamnan jihar Kano, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, ya ce rikicin cikin gida da ya dabaibaye jam’iyyar PDP ya na iya tarwatsa jam’iyyar baki daya ta mutu murus.

An ruwaito cewa Sanata Kwankwaso ya ce ba a bukatar irin wannan rikicin a wannan lokacin da jam’iyyar ke fama da rasa mambobin ta daga sassa daban-daban a kasar.

A yayin zantawa da BBC Hausa, Kwankwaso ya ce tuni ya nesanta kan sa daga dukkan wani rikici kuma kamar yadda ya ce, wadanda ba kwararrun ‘yan siyasa ba ne suka hura wutar.

“A yanzu karfin jam’iyyar ya ragu kuma a karshe abinda zai faru shi ne za mu tarwatse baki daya.” “Ka ga wannan sakamakon ba zai taimake mu ba saboda ba mu da shugaban kasa kuma ba mu da gwamnoni masu yawa,”.

Ya shawarci shugabannin jam’iyyar da su mayar da hankali kan jama’arsu da yadda za su taimake su. “Mutum kamar ni ba shi da wata alaka da rikici. Ni ina duban abinda zai kawo ci gaba ne ga jama’a, abinda kowanne shugaba na gari zai mayar da hankali a kai.”

“Shugaban jam’iyya yanzu wata daya ya rage masa. A tunani na, zai fi idan ya tsaya ta yadda za mu bayyana da karfinmu. “Amma wannan rikicin na habaka ne da taimakon wadanda suke son shugabanci. Ba don damuwar jama’a su ke yi ba,”.

Related posts

Leave a Comment