Gwamnoni 36 na Najeriya za su yi taro a yau Laraba 4 ga watan Nuwamba 2020 a kan yadda za su shawo kan matsalolin da ke addabar Najeriya, biyo bayan Zanga-Zangar EndSARS wadda ta rikide zuwa sace-sace da lalata dukiyar gwamnati.
Gwamnonin za su yi amfani da damar don tattaunawa a kan yadda za a yi da rundunar SARS da aka rushe, wadanda ayyukansu suka yi sanadiyyar zanga-zanga a cikin jihohin Najeriya. Sannan za su tattauna a kan yadda aka wawushe kayan tallafin COVID-19 a ma’ajiyoyin gwamnati da ke jihohi daban-daban.
Babban Darakta Janar na ?ungiyar gwamnonin Najeriya Ashishana Bayo Okauru, ya ce shugaban kungiyar gwamnoni, gwamnan jihar Ekiti, Dr John Kayode Fayemi, zai yi jawabi a kan matsalolin da ke addabar Najeriya kuma suke haifar da barazana ga wanzuwar zaman lafiya a fa?in ?asar.
Okauru ya ce gwamnan jihar Ekiti zai tattauna da takwarorinsa na jihohi a kan yadda suka yi da fadar shugaban kasa a kan UBEC, don yanzu haka makarantu sun fara budewa a jihohi.
Ya ?ara da cewar Dr Fayemi zai yi magana a kan abubuwan da gwamnoni suka tattauna a shagalin cikar Gidan Arewa shekaru 50 wanda aka yi cikin karshen mako a cibiyar Arewa wato jihar Kaduna.
Darakta janar na ?ungiyar gwamnonin yace, ana bukatar ganin gwamnonin da misalin karfe 1 na rana, sannan za’a fara taron da misalin karfe 2:00 na rana daidai, a birnin tarayya Abuja.
