Rahotannin dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar hukumomin birnin sun yi nasarar cafke wasu mutane 480 da ake zargin fursunoni ne da suka tsere daga gidan Kurkukun kuje daga gine-ginen da ba a karasa ba da kangwaye a yankunan Maitama da Wuse II.
Shugaban jami’an kar-ta-kwana da ke farautar fursunonin, Mista Bennett Igweh, ya ce fursunoni da galibinsu maza ne sun mayar da kwangaye da gidajen da babu mutane da filaye maboya domin cigaba da aikata muggan laifuka.
Ya kuma kara da cewa jami’an sun kuma kama mutanen dauke da kakin ‘yan sanda da wayoyin hannu da bindiga da adduna da wasu irin makamai.
Jami’in ya ce za su cigaba da kai wannan samame a matsugunai 21 na marasa karfi da suka hada da Kabusa da Gishiri da Waru da Wasa da sauransu da ke cikin garin Abuja.
Igweh ya ce sun alkawarta kawo karshen irin wadannan miyagu da ke haifar da barazanar tsaro a Abuja.
