2023: Zan Taimaka Wajen Kifar Da PDP – Martanin Wike Ga Shugaban PDP

Rahoton dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar gwamnan jihar Ribas Wike ya sha alwashin sa hannu wajen faduwar jam’iyyar PDP a za?en shugaban kasa na 2023.

Wike na martani ne game da kalaman da shugaban jam’iyyar PDP ya yi yayin wata hira da BBC Hausa, inda ya ce ”masu kiraye-kirayen ya saukan yara ne da ba su fahimci manufofin kafa jam’iyyar ba”.

Gwamna Wike ya kara da cewa ”Na yi tunanin a matsayinka na shugaban jam’iyya wanda ke son jam’iyyarsa ta yi nasarar lashe zabuka, bai kamata ka yi abin da zai raba kawunan ‘yan jam’iyya, haka kuma bai kamata ka nuna wa jam’iyya girman kai ba”.

Ya ci gaba da cewa ”Hakika yaran ne suka kawo ka matsayin shugaban jam’iyya, kuma yaran ne suka dauko ka daga cikin talaucin da kake fama da shi, muka mayar da kai matsayin shugaban jam’iyyarmu, amma yanzu mun fahimci cewa so kake yi jam’iyyar ta fadi zabe, to lallai za mu taya ka”

Related posts

Leave a Comment