Kurakuran PDP Ne Silar Zaman Buhari Shugaban Kasa – Saraki

Tsohon shugaban majalisar dattawa Bukola Saraki ya alakanta hawan Buhari da jamiyyar APC mulki da kura-kuran da jam’iyyar PDP ta tafka.

Saraki ya bayyana matsayinsa ne ta hannun Farfesa Iyorwuese Hagher, shugaban kungiyar yakin neman shugabancinsa, lokacin da ya jagoranci tawagarsa zuwa Dutse babban birnin jihar Jigawa don tattaunawa da masu ruwa da tsaki na PDP a jihar.

Ya ce mafita kwaya daya da ya rage ma jam’iyyar adawar shine ta yi aiki don kwato shugabancin kasar domin kawo ainahin chanjin da kasar ke muradi.

Tsohon shugaban majalisar dattawan na daya daga cikin masu neman takarar shugaban kasa karkashin PDP a 2023, tare da tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar da kuma gwamnan jihar Sokoto, Aminu Tambuwal da sauransu.

Hagher ya ce: “Mun yarda cewa Najeriya ta cancanci shugaba da zai iya hada kanta. “Muna sane kuma mun damu sosai da halin da kasar ke ciki a yau, ta yadda aka banzatar da hadin kanmu.

Ya yi takaici cewa saboda raunin PDP a 2015, yan Najeriya suka zabi APC, wacce bata da wata manufa ga kasar, inda ya kara da cewa: “Da ace ‘ya’yan PDP basu karya martabarta ba da kuma hadewa da wasu kungiyoyi da suka zo suka kwace mulkiba da APC bata taba mafarkin hawa mulki ba.

“Sun karbi mulki kuma muna iya ganin cewa basu da kowane ajanda sai dai azabtar da yan kasa. “A yau babu wanda ya tsira, babu wanda ke murna saboda mune tushen talauci a duniya karkashin gwamnatin APC, mune kasa da ke da mafi yawan yara da basa zuwa makaranta, inda makomarmu ta zama wani iri.”

Related posts

Leave a Comment