Rahotanni daga Jihar Katsina na bayyana cewar Mai martaba sarkin Katsina, Alhaji Abdulmumini Kabir, ya nuna goyon bayansa ga takarar Sanata Ahmed Bola Tinubu na shugabancin kasa.
Ya bayyana hakan ne yayin da ya ke tarbar wata tawagar kungiyoyin Arewa masu goyon bayan takarar shugabancin kasar Tinubu da suka kai masa ziyara a fadarsa a ranar Juma’a a Katsina.
Sarkin ya ce Tinubu ya cancanta kuma zai shayar da ?an Najeriya romon demokradiyya, “Tinubu mutum ne da zai iya ceto yan Najeriya daga matsalolin tsaro, tattalin arziki da zamantakewar. “Na san Tinubu tsawon shekaru saboda yana da kusanci da mahaifi na, Marigayi Sarkin Katsina, Alhaji Muhammad Kabir Usman.”
“Muna ?aukan Tinubu tamkar ?an asalin Jihar Katsina ne saboda alaka mai tsawo da muke da shi. “Muna goyon bayan sa ?ari bisa ?ari,” in ji shi.
Sarkin ya yi kira ga sauran yan Najeriya su mara wa Tinubu baya saboda kwarewarsa.
Tunda farko, Shugaban tawagar, tsohon dan majalisar Dattawa, Sanata Abu Ibrahim ya shaidawa Sarkin cewa suna zagayawa ne domin neman hadin kan yan Najeriya su goyi bayan abokinsu da suke koyi da shi. Abu Ibrahim ya yi alkawarin cewa Sanata Tinubu zai warware matsalolin Najeriya idan an zabe shi shugaban kasa.
