Fafaroma Ya Yi Kiran Kawo Karshen Yakin Rasha Da Ukraine

Fafaroma Francis, ya yi kiran da a dauki kwararan matakai na kawo karshen yakin da ake a Ukraine da kuma kaucewa fada wa masifar nukiliya a Zaporizhzhia.

Da ya ke jawabi a yayin taron mako-makon da yake da mabiyansa, Fafaroman ya yi alawadai da yakin da ya kira rashin hankali, da kuma bayyana kisan da aka yi wa Darya Dugina, a matsayin rashin imani.

Fafaroman ya ce yana so ya kai ziyara Kyiv to amma yana so ya fara zuwa Moscow ne da farko don kawo karshen yakin.

Ya?in kasashen biyu dai ya jefa tattalin arzikin duniya cikin wani yanayi abin da masana ke fa?in idan ba a tsayar dashi ba matsalar za ta munana.

Related posts

Leave a Comment