Kungiyar Afenifere Ta Yi Tir Da Zaben Tinubu

Pa Ayo Adebanjo, shugaban kungiyar Yarabawa ta Afenifere, ya mayar da martani kan ayyana ?an takarar shugaban ?asa na jam’iyyar APC, Bola Ahmed Tinubu a matsayin wanda ya lashe za?en shugaban ?asa.

Yayin da yake magana a wata tattaunawa ta wayar tarho da BBC, Adebanjo ya bayyana za?en da ya bai wa Tinubu nasara a matsayin mai cike da kura-kurai.

Ya ce sakamakon za?en shugaban ?asa ba abu ne da za a amince da shi ba, kuma hakan na iya haifar rikici a ?asar.

Adebanjo ya ce gazawar da INEC ta yi na amfani da na’urar BVAS a rumfunan za?e kamar yadda ta yi alkawari tun da farko, ya nuna cewa wasu sun tsara yadda za?en zai gudana da kuma ?an takara da suke so ya yi nasara.

Ya ?ara da cewa a iya saninsa, shi dai ba a gudanar da za?e a ?asar ba a ranar Asabar ?in da ta gabata.

“Wannan ba za?e ba ne kuma duk mun san haka, a fili ta ke cewa an tafka magu?i kuma hakan ba abin yarda ba ne.

“Hakan ba zai yiwu ba, su waye ke aika sakon taya murna ga za?ab?en shugaban ?asa? Har yanzu ba mu gudanar da za?en shugaban ?asa ba.”

Adebanjo ya bayyana cewa ba jam’iyyarsa ta siyasa ce ka?ai ta yi Allah-wadai da sakamakon za?en shugaban ?asa ba, har ma da masu sa-ido na cikin gida da na waje da suka shaida yadda za?en ya gudana da ma ?aukacin jam’iyyun adawa ba su ji da?in yadda za?en ya gudana ba.

Related posts

Leave a Comment