Rahotanni dake fitowa daga ?asar Indiya, sun nuna cewa hukumomi sun cafke, Aryan Khan, ?an shararren jarumi, Sharukh Shah Rukh Khan, ranar Lahadi.
BBC Hausa ta ruwaito cewa jami’an hukumar (NCB), masu sanya ido kan masu shan miyagun kwayoyi, sun dam?e Aryan Khan ne bisa zarginsa da shan miyagun kwayoyi yayin wata liyafa ta nisha?i.
Khan ya shiga hannu ne yayin da yake kan hanyarsa ta zuwa Goa daga Mumbai, tare da iyalansa a cikin wani jirgin ruwa.
Jami’an hukumar NCB, da suka jagoranci damke Aryan Khan, sun bayyana cewa sun ?auki wannan matakin ne ?ar?ashin doka, “Mai alaka da sha da fataucin miyagun kwayoyi.”
Hakanan masu sharhin na ganin cewa babu wani kwakkwaran dalili na tsare Khan duba da takardun da suka bayyana na cafke shi.
