Labarin dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Jam’iyyar New Nigeria Peoples Party (NNPP) mai kayan marmari tayi kira da a soke sakamakon za?en shugaban ?asa na 2023.
Jam’iyyar tayi wannan kiran ne a wani taron manema labarai da shugaban ta na ?asa, Rufai Alkali, yayi a birnin tarayya Abuja.
Alkali yace yadda INEC ta gudanar da za?en shugaban ?asar, hukumar ta mayar da ?asar nan baya wajen yin irin za?ukan da akeyi kafin shekarar 2015. “Mun damu matu?a kan abubuwan da suka faru ranar za?e, hukumar za?en ta mayar da ?asar mu baya wajen yin irin za?ukan da akeyi kafin shekarar 2015, inda akeyin abinda aka ga dama, a hana masu ka?a ?uri’a za?e.”
“Satar akwatunan za?e, inda ake takurawa masu ka?a ?uri’a, siyan ?uri’u da rigingimu sune abin da ke sanyawa a lashe za?e, inda jami’an tsaro suke komawa bayan jam’iyya mai mulki su taimaka tayi magu?i a bainar jama’a.”
Alkali ya lissafo wasu muhimman abubuwa bakwai da jam’iyyar su ta lura da su akan za?en sune, INEC da gangan ta hana NNPP sakewa a za?en, ta kyale shugaba Buhari da wasu yin kamfen ranar za?e, hana masu ka?a ?uri’a yin za?e, Siyan ?uri’u, lalacewar na’urar BVAS da aringizon ?uri’u, ?arya kan IREV da za?e wanda rigingimu suka yi yawa a cikin sa.
A dalilin haka, sai yayi kira da a soke za?en na shugaban ?asa “Domin ceto dimokuradiyyar mu da ?asar mu, ?an Najeriya da ?awayenta dole ne su ?i yarda da wannan sakamakon za?en.”
