Sana’ar Shayi Na Gada Ba Waka Ba – Ado Gwanja

Shahararren Mawakin finafinai Hausa mazaunin Birnin Kano Ado Gwanja, ya bayyana cewar Allah ya nufa zai ci abinci ta hanyar wakane, amma abin da ya gada daga wajen mahaifinsa shine sana’ar dafa Shayi.

Gwanja ya bayyana hakan ne a yayin tattaunawa da gidan rediyon BBC Hausa ya yi dashi a cikin shirin Daga Bakin Mai Ita.

Mawakin ya bayyana cewar Mahaifinsa ?wararre ne a fuskar sana’ar Shayi, domin a zamanin marigayi Sarkin Kano Ado Bayero Mahaifin nashi shine ke dafawa mai Martaba Shayi na musamman.

Ado Gwanja ya tabbatar da cewar sana’ar waka ta yi mishi komai, domin ya samu arziki da ita, a ciki ya yi gida yayi aure yayi abin hawa, Saboda haka babu abin da zai ce sai dai godiya ga Allah.

Mawakin ya bayyana cewar a rayuwarsa yana tsananin son zuwa kasashen Turai, saboda tsari da wayewarsu a rayuwa. Daga karshe ya yi godiya ga dinbin masoya da yake dasu a gida da waje, wa?anda ya bayyana cewar da bazarsu yake rawa.

Related posts

Leave a Comment