An Damke Wanda Ya Tsokani ‘Yar Gwagwarmaya Kan Auren Malala

Hukumar Tsaro ta Farin Kaya, SSS, ta kama wani mai amfani da kafar facebook, Ibrahim Sarki Abdullahi sakamakon tsokanar ?ar gwagwarmayar nan mai rajin kare ha??in mata, Zainab Nasir a kan ra’ayinta kan aure.

Wata majiya daga hukumar ta baiyanawa jaridar DAILY NIGERIAN cewa Abdullahi na nan ya na shan tuhuma a kan yadda ya ke tsokanar mutane a kafar sadarwa.

Tun a baya ne dai Zainab ta ta?a baiyana matsayinta a kan aure, in da ta ce “aure ba nasara ba ne”, batun da ya haifar da cecekuce a kafafen sadarwa.

Haka-zalika a ranar da Malala Yousafzai ta baiyana yin aurenta, jama’a da yawa sun tuna Zainab a kan matsayinta kan aure.

Idan za a tuna, a kwanannan ne dai Abdullahi ya wallafa hoton Zainab ?in a facebook tare da wani sa?o da ya ke cewa “Malala ta shushe mu”, lamarin da ya kufular da ?ar rajin kare ha??in mata ?in har ta yi barazanar maka shi a kotu.

Amma daga bayan, bayan Zainab ta yi barazanar maka shi a kotu, sai Abdullahi ya yi wuf ya goge sa?on, amma ina, ha?ar shi ba ta cimma ruwa ba, don tuni jami’an farin kaya su ka cafke shi.

Related posts

Leave a Comment