Kotu Ta Jingine Hukuncin Sauke Sifeton ‘Yan Sanda Daga Mukaminsa

Babbar Kotun tarayya mai zama a Awka, babban birnin jihar Anambra ta jingine hukuncin tsige Usman Baba daga matsayin sufetan ‘yan sanda na ?asa (IGP).

An ruwaito cewa yayin yanke hukunci ranar 19 ga watan Mayu, Alkalin Kotun, mai shari’a Fatun Riman, ya umarci Baba ya daina ayyana kansa a matsayin IGP.

Da yake kalubalantar hukuncin a gaban Kotun, IGP ta hannun lauyansa, ya shaida wa Alkalin cewa ba’a masa adalci ba a sauraron ?arar saboda mai ?ara ya gaza kai masa takardar sammaci ta usuli.

Related posts

Leave a Comment