Ina Neman Afuwar Musulmi Kan Kalaman Da Na Yi – Kashim Shettima

Maitamakin shugaban Najeriya Sanata Kashim Shettima ya ce yana neman afuwan al’ummar Musulmi bisa wadansu kalamai da ya yi kan za?en shugabannin majalisar dokokin Najeriya.

A cewarsa ba a fahimci maganar a sigarta ba, kuma ba shi da wata manufa na ?ata sunan addininsa.
Sanata Kashim a tattaunawarsa da BBC ya ce ya yi wa?annnan maganganu ne saboda maslahar Najeriya, ganin cewa suna da wasu bayanai na sirri da bai dace ya fito yana fa?i ba.


Sannan yadda lamura ke tafiya a Najeriya a wannan lokaci, dole shugabanni su fito su ja hankali domin wanzuwar kasar baki-?aya.
Kalaman Shettima a cikin makon da ya gabata ya haifar da zazzafar muhawara musamman a shafukan sada zumunta inda aka rin?a sukar mataimakin shugaban kasar.

Sai dai Kashim Shettima ya ce shi Musulmi ne na ha?i?a domin zuri’arsu sun shafe tsawon dubban shekaru kan tafarkin addinin Islama.
Sannan duk wanda bai jidadin kalamansa ba, ya yi hakuri a yafe masa, ba shi da niyyar cutar da addini.
“Ni ?an adam ne kuma ajizi don haka ina neman afuwan al’umma da Ubagijina”.

Kashim Shettima ya tunasar da cewa shi ?an malamai ne kuma jikan malamai, don haka ba shi da niyyar muzantawa wani ?angare na addinin kasar.

Related posts

Leave a Comment