Labarin dake shigo mana daga birnin Abeakuta na Jihar Ogun na bayyana cewar Tsohon shugaban ?asa Olusegun Obasanjo ya yi magana kan tazarcen da ya so ya yi karo na uku wanda bai yi nasara ba lokacin yana kan mulkin ?asar nan a karo na biyu.
Idan ba a manta ba a shekarar 2006, an kai wani kudiri gaban majalisar tarayya domin yi wa kundin tsarin mulkin shekarar 1999 gyara da ?ara wa’adin mulki, ?udirin da aka ?i amincewa da shi.
Obasanjo ya bayyana cewa akwai hannun wasu gwamnonin jihohi a cikin tazarcen karo na uku saboda suna son su yi hakan a jihohinsu, shi yasa suka matsa mishi domin ya amince da yin tazarcen.
Da yake magana a yayin tattaunawa da wani gogaggen ?an jarida, Chude Jideonwo, tsohon shugaban ?asar ya bayyana cewa wasu gwamnonin sun so ?ara wa’adin mulkinsu da shekara hu?u.
Da yake magana kan tazarcen nasa wanda bai yiwu ba, Obasanjo ya bayyana cewa: “Gwamnonin, wasu daga cikinsu saboda kansu su ke yi.” “Saboda idan shugaban ?asa ya yi mulki a karo na uku, su ma za su samu damar yin mulki sau uku.”
Da yake magana kan zarge-zargen salwantar da dukiyar ?asa da ake masa, Obasanjo ya bayyana cewa ya ?ware ne a wajen samar da ku?i ba salwantar da su ba. Ya bayyana cewa mutanen da ba za su iya yin abubuwan da ya yi ba, su daina sukar shi.
