Kotu Ta Bukaci Masu Kalubalantar Tinubu Su Biya Miliyan Goma-Goma

Rahotannin dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar babbar kotun tarayya ta yi watsi da ?arar da wasu mazauna birnin suka shigar a gabanta suna neman ta hana rantsar da shugaban ?asar Bola Ahmed Tinubu.

Yayin da yake yanke hukuncin ranar Talata, al?alin kotun, Mai shari’a Inyang Ekwo, ya umarci masu ?arar da kowannensu ya biya naira miliyan 10 ga ministan shari’a kuma Atoni janar na ?asar.

Masu ?arar dai na i?irarin cewa shugaban ?asar Bola Tinubu bai samu samu kashi 25 cikin 100 na ?uri’un da aka ka?a a baban birnin tarayyar Abuja, dan haka suke ganin bai cancanci zama shugaban ?asar ba.

Mai shari’a Ekwo ya ce masu karar ba su da ‘yancin shigar da ?arar a kotun, yana mai cewa a gaban kotun sauraron ?orafe-?orafen za?e ne kawai ya kamata a shigar da ?asar, a maimakon babbar kotun tarayyar da ke Abuja.

Related posts

Leave a Comment