Rahotannin dake shigo mana daga birnin Ilori na Jihar Kwara na bayyana cewa gwamnatin jihar ta amince da ?aukar matakin wucin-gadi na rage adadin kwanakin aikin gwamnati a jihar domin rage wa ma’aikata ra?a?in da janye tallafin man fetur zai haifar.
Wani sa?o da sakataren ya?a labaran gwamnan jihar Murtala Atoyebi, ya fitar kuma aka wallafa a shafin gwamnatin jihar na Facebook, ya ambato shugabar ma’aikata a jihar, Mrs Susan Modupe Oluwole na bayyana matakin,
Mrs Oluwole ta ce gwamnan jihar Abdulrahman Abdulrazaq ne ya bayar da umarnin rage kwanakin aikin gwamnatin na wucin-gadi daga kwana biyar zuwa uku a kowane mako.
Mrs Oluwole ta umarci shugabannin ma’aikatu da hukumomin gwamnati da ke fa?in jihar su gaggauta tsara wa ma’aikatansu kwanakin da ya kamata su je aiki.
Shugabar ma’aikatan jihar ta kuma garga?i ma’aikatan kada su tozarta wannan karamci da gwamnan jihar ya yi musu, tana cewa za a tsananta lura da kai ziyara ma’aikatu domin tabbatar da cewa ana bin dokar yadda ya kamata.
