Gwamnoni Sun Goyi Bayan Janye Tallafin Mai Da Tinubu Ya Yi

Gwamnonin jihohin Najeriya sun nuna goyon bayansu ga matakin da shugaban ?asar Bola Ahmed Tinubu ya ?auka na cire tallafin man fetur.

Gwamnonin sun bayyana haka ne a lokacin wata ganawa da suka yi da shugaban ?asar a ranar Laraba.

Wata sanarwa da ta fito ta hannun daraktan ya?a labarai na fadar shugaban Najeriya, Abiodun Oladunjoye, ta ce gwamnonin sun rin?a yin jawabi ?aya bayan ?aya a lokacin ganawar, inda suka rin?a yaba wa shugaban ?asar kan matakin da ya ?auka.

Gwamnonin wa?anda suka je fadar bisa jagorancin shugaban ?ungiyar gwamnonin Najeriya kuma gwamnan jihar Kwara, AbdulRahman AbdulRazaq sun ce za su yi aiki tare da shugaban ?asar wajen ganin an magance matsalolin da cire tallafin zai haifar.

Shugaba Bola Tinubu ne ya sanar da ?arshen tallafin man fetur a ranar 29 ga watan Maris, lokacin da ya sha rantsuwar kama aiki.

Ya ce gwamnati za ta karkatar da ku?a?en tallafin zuwa ga wasu ?angarori na ci gaban ?asa.

Sai dai ?ungiyoyin ?wadago na ?asar sun nuna adawa da lamarin, inda suka yi yun?urin shiga yajin aiki, amma daga baya an cimma matsaya bayan jerin tattaunawa tsakanin gwamnati da ?ungiyoyin na ?wadago.

Related posts

Leave a Comment