Rahotannin dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Jam’iyyar APC mai mulki ta yanke shawarar ba yankin arewacin mu?amin shugaban jam’iyyar na ?asa yayin da ake tunkarar babban za?e na 2023.
Gwamnan Jihar Kaduna Nasir Ahmed El-Rufai ya fa?a wa manema labarai hakan jim ka?an bayan ganawarsu da Shugaba Muhammadu Buhari ranar Talata, cewa jam’iyyar ta amince ta rarraba mu?aman da babu kowa a kai a Kwamatin ?oli na jam’iyyar tsakanin Kudu da Arewa kafin babban taronta na ?asa.
Hakan na nufin mu?amin shugabancin wanda John Odigie-Oyegun da Adams Oshiomhole suka ri?e a baya, dukkansu ‘yan Kudu, zai koma Arewa.
“Mun amince da wani tsari na karkasa mu?amai ga dukkan shiyyoyin siyasa. Shiyyoyin Arewa za su samu mu?aman da na Kudu suka ri?e a cikin shekara takwas da suka wuce, su ma (na Kudu) haka,” a cewar Gwamna El-Rufai.
Yayin taron, gwamnonin jam’iyyar ta APC sun amince da sabon lokacin da jam’iyyar ta za?a don gudanar da babban taronta na ?asa duk da cewa an samu rabuwar kai tsakaninsu.
Gwamna El-Rufai ya ce ba zai yiwu a tara gwamnoni har 22 ba “kuma a ce ba a samu bambancin ra’ayi ba”.
Ranar Litinin ne kwamatin ri?o na shugabancin jam’iyyar ya bayyana cewa ya fasa gudanar da babban taron a ranar 26 ga watan Fabarairu sannan ya mayar da shi 28 ga Maris.
“An samu bambancin ra’ayi tsakanin gwamnonin APC game da lokacin taron,” in ji El-Rufai kamar yadda mai bai wa Shugaba Buhari shawara kan kafafen sada zumunta Tolu Ogunlesi ya ruwaito shi yana fa?a.
Ya ?ara da cewa: “Wannan kuma wai shi ‘yan jarida ke kira gwamnoni marasa ha?in kai. Babu yadda za a yi a tara gwamnoni 22 kuma kowa ya amince da kowane irin ?udiri. Za a iya samun bambanci amma idan aka kira shi rabuwar kai to an wuce gona da iri.”
Baya ga sabuwar ranar gudanar da babban taron, APC ta shaida wa hukumar za?e ta INEC cewa za ta fara gudanar da taron na shiyya-shiyya tukunna daga ranar 6 ga watan Maris, inda za a za?i shugabanni a matakin shiyya.
Jim ka?an bayan ganawar da suka yi da Buhari, Gwamna El-Rufai ya ce gwamnonin sun amince da wani tsari “na adalci” ga kowane sashen siyasa na Najeriya.
“Bayan ganawarmu da shugaban ?asa a ranar (Talata), mun ha?u a kan abu ?aya. Mun amince da wani tsari mai adalci da kuma ingantacciyar hanyar rarraba mu?amai ga dukkan sashen siyasa,” a cewarsa.
“Cikin ikon Allah nan da 26 ga watan Maris za mu gudanar da babban taro na ?asa.
“Babu wata tantama cewa kan gwamnonin APC a ha?e yake wajen yun?urinmu na tabbatar da cewa PDP ba ta dawo kan mulki ba.”
