EFCC Ta Sake Bankado Zunubban Tsohon Akanta Janar


Hukumar EFCC ta ce a yau Juma’a za ta gurfanar da tsohon Akanta-Janar, AGF na Tarayya, AGF, Ahmed Idris.

Wilson Uwujaren, babban jami’in yada labarai na EFCC ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar a jiya Alhamis, a Abuja

Uwujaren ya ce za a gurfanar da tsohon AGF ?in tare da wasu mutane uku a gaban mai shari’a Adeyemi Ajayi, na wata babbar kotun birnin tarayya Abuja.

Ya ce sauran ukun da aka kama tare da AGF ?in a kan zargin sama-da-fa?i da sama da Naira biliyan 109 sun ha?a da Godfrey Akindele, Mohammed Usman da Gezawa Market and Exchange Limited.

A cewarsa, za a gurfanar da wadanda ake zargin ne a gaban kuliya bisa tuhume-tuhume 14 da suka hada da sata da kuma cin amana da ya kai N109,485,572,691.9.

Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya ya tuna cewa hukumar EFCC ta kama tsohon AGF ne a ranar 16 ga watan Mayu, bisa zargin karkatar da kudade da kuma almundahanar da Naira biliyan 109.

Hukumar EFCC ta ce rahotannin sirri da aka tabbatar sun nuna cewa Idris ya kwashe kudaden ne ta hanyar wasu ayyuka na bogi da kuma wasu ayyuka da suka sabawa doka ta hanyar amfani da wasu makusanta, ‘yan uwa da abokai.

Hukumar ta ce an karkatar da kudaden ne ta hanyar zuba jari a Kano da Abuja.

Related posts

Leave a Comment