Kisa Ne Maganin ‘Yan Ta’adda Ba Sulhu Ba – El Rufa’i

A daidai lokacin da ‘yan bindiga ke ci gaba da kai hare-hare babu kakkautawa a jihohin Arewa, Gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai ya ce rashin hadin kai tsakanin gwamnonin yankin na da daga cikin abin da ya sa aka kasa shawo kan matsalar.

A hirarsa da BBC gwamnan ya ce shi yana da ra’ayin a bude ma ‘yan bindigar wuta kuma babu batun sulhu tsakanin gwamnatinsa da masu garkuwa da mutane.

Kalaman El Rufa’i na zuwa ne bayan jawabin da sanannen malamin addinin Musulunci Dr. Ahmad Gumi ya yi, inda ya yi kira ga gwamnati da ta yi sulhu da ‘yan Bindiga.

Furucin El Rufa’i ya zama wani abin tafka mahawara a tsakanin ‘yan Najeriya, inda wasu ke goyon bayan kalaman gwamnan, yayin da wasu suke suka.

Related posts

Leave a Comment